Magoya bayan Akpabio sun yi jana’izar PDP


Magoya bayan tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio wanda ya sauya sheka ya zuwa jam’iyar APC mai mulki sun yi jana’izar jam’iyar ta PDP.

Yayin wani taron gangamin karbarsa da aka gudanar ranar Laraba wasu magoya bayan sanatan sun dauki akwatin gawa dake dauke da tutar jam’iyar a PDP.

Mutane da dama ne suka halarci taron gangamin da ya gudana a filin wasa na Ikot Ekpene.

A cikin manyan bakin da suka halarci taron har da shugaban jam’iyar APC na kasa Adam Oshimhole, Bola Ahmad Tinubu da kuma wasu sanatocin jam’iyar ciki har da shugaban masu rinjaye sanata Ahmad Lawal.

Sauya shekar ta Akpabio daga jam’iyar PDP ta zowa mutane da dama da bazata.

Sai dai wasu daga cikin sanatocin jam’iyar ta PDP sun bayyana shi a matsayin matsoraci.


Like it? Share with your friends!

1
111 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like