Mafusata Sun Kashe Barawon Babur, Yayin Da ‘Daya Ya kubuta Da ‘Kyar


A cikin jihar Katsina an biyo wani barawon mashin tin daga Sabon Layi ake biye da shi har zuwa unguwar Koren Dorowa, barawon tafiyar da yayi za ta iya daukar nisan kilomita biyar ‘yan acaba na biye da shi da mashina.

Barawon yana shirin kama hanyar zuwa dutsinma road ne yaga gungun mutane da yawa sun cika titin, a tunaninsa zaisa wasu sunyi waya ne a tare wurin da zai wuce, to ashe daman wani ‘barawon mashin dinne banda shi, da yaga mutane da itace a hannunsu kawai sai ya danna birki ya dire daga kan mashin din, ya shiga lungu da gudu. Shigarsa lungu ke da wuya masu biye da shi a mashinan nan suka biyoshi, suka hau kanshi suka takashi, haka suka rinka dukansa har saida ya mutu.

Gudan ‘barawon kuma da yaji ana cewa “ga gudan barawon nan shi ma a kashe shi”, Kawai sai ya ruga cikin wani shago mai bagala ya turo shagon ya rufe, Saboda kar a kashe barawon a cikin shagon a jawa mai shagon matsala, ‘yan unguwa sukai bakin kokarinsu, suka rufe shagon da kwado, suka ce mai shagon ya gudu. Mafusatan matasan sukai yunkurin fasa shagon domin su fiddo barawon su kashe, kafin su fasa bagalar shagon, Aka kira ‘yan sanda suka zo domin su tafi da ‘barawon da aka kashe da kuma wanda ba a kashe ba.

Daga bisani ‘yan sanda sun zo sun tafi da gawar tare da tarwatsa jama’a.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 9

Your email address will not be published.

You may also like