Mafarauta Sun Sami Nasarar Kame Kada Mafi Girma A Duniya


Wasu mutane mafarauta namun ruwa a kasar Australia sun kama wata Kada ma tsawon takun kafa 15 kwatan kwatankwacin mita 4.7, wadda masana suka bayyana Kadar a matsayin wadda tafi kowace halitta dake jan ciki tsayi da kuma karfi a duniya.

Mafarautan dai sun bayyana cewa shekara 8 kenan suna neman Kadar tare da dana mata tarko domin su kamata amma abun yaci tura sai yau.

Mafarautan sun bayyana shekarun Kadar da suka kama a Arewacin kogin Katherine dake kasar Australia 60 a duniya kuma sun bayyana cewa tun shekarar 2010 suke son su kama Kadar domin canza mata mazauni amman sai yau suka samu wannan babbar nasarar.


Like it? Share with your friends!

-7
81 shares, -7 points

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like