Maciji Ya Laƙume Milyan 36 Na Kudaden Jarrabawar Shiga Jami’a


Wata Ma’aikaciyar hukumar shirya jarrabawar shiga jami’a ( JAMB), a jihar Binuwai, Misis Philomina Chieshe ta bayyanawa Shugaban hukumar cewa wani maciji ya lakume Naira milyan 36 na kudaden cinikin katin jarrabawar wanda aka yi.

Ma’aikaciya wadda ita ce ke sayar da katin ta nuna cewa macijin ya kasance yana shiga cikin ofishin ne a akai akai inda ya hadiye wadannan kudaden wadanda aka adana su a cikin ofishin. Sai dai, wannan bayanin bai gamsar da Shugaban hukumar wanda ake ganin zai dauki mataki wajen ganin inda kudade suka makale.


Like it? Share with your friends!

-2
85 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like