Hukumomin kasar Pakistan sun nunar da cewa adadin wadanda suka mutu a hadarin jirgin kasa na iya karuwa saboda da yawa daga cikin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali. A ranar Litinin ne wani jirgin kasa na fasinja ya ci karo da wani jirgin da ya kauce wa hanya a kusa da garin Daharki a lardin Sindh.

Kimanin mutane dubu da 200 ne ke cikin jiragen biyu da suka ci karo da juna. Sai dai hadarin jirgin kasa dai na neman zama ruwan are a kasar Pakistan, sakamakon rashin sabunta layin dogo da rashin kyakkyawar tsari na tafiyar da sufurin jiragen kasa.