Mabiya Shi’a Sun Yi Gagarumar Zanga-zangar Lumana A Abuja Saboda Hana Belin Zakzaky Da Kotu Ta Yi A Yau


Rahotanni daga Abuja sun bayyana yadda mabiya Mazhabar Shi’a Almajiran Shaik Ibraheem Zakzaky suka yi wani gagarumin maci da yammacin yau Laraba a birnin tarayya Abuja.

Sun gudanar da zanga-zangar mai taken ‘Bamu Yarda da Kotu ba’ suna masu bayyana cewa rashin bada belin Shaik Ibraheem Zakzaky da alkali yayi yau hakan rashin adalci ne. Idan ba’a manta bade yau ne akayi zaman sauraron karar wanda daga bisani alkali yaki amincewa da bada belin Shaik Zakzaky kaman yanda lauyan sa ya nema.

Alkalin ya daga zaman zuwa ranar 22/01/2018 domin sauraron shaidu daga bangare biyu da kuma yiyuwar bada belin ko kuma yanke hukunci. Har zuwa kammala wannan rahoto bamu samu bayani daga bangaren gwamnatin jihar Kaduna ba, wacce ta shigar da karar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like