Mabiya Shi’a sun yi barazanar sauya salom zanga-zanga idan har gwamnati ta gaza sakin Elzakzaky


Mambobin kungiyar yan uwa musulmi wacce akafi sani da Shi’a sun gudanar da wani jerin gwano a birnin tarayya Abuja domin tunawa da ranar da aka haifi, Ibrahim Elzakzaky jagoran mabiya darikar ta Shi’a a Najeriya.

Elzakzaky na tsare a hannun hukumar tsaro ta farin kaya tun bayan da aka kama shi a watan Disambar shekarar 2015.

A yanzu haka dai yana fuskantar tuhume-tuhume a gaban kotu da suka hada da gudanar da taro ba tare da bin doka ba, da kuma tayar da hankalin al’umma.

Magoyae bayansa sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake shi.Inda suka yi barazanar canza salo idan har gwamnati ta cigaba da tsare shi.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like