Ma’aikatan Lantarki Zasu Shiga Yajin Aiki A Arewa Maso Gabas


An baiwa kamfanin rarraba hasken wutan Lantarki dake Jihohin Borno, Adamawa, Yobe, da kuma jahar Taraba wa’adin sa’o’i 24 da ya biya ma’aikata hakkokinsu ko kuma ya fuskanci yajin aiki na illa masha Allah.

Hakan ya biyo bayan zanga zangan lumana da hadakar kungiyar ma’aikatan sukayi a ofishin kamfanin dake Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.

Nasiru Dambo wanda shine mai magana da yawun hadakan kungiyar ma’aikatan kamfanin rarraba wutan lantarki yace in harfa ba a sanya hannu kan kundin tsarin aikin kamfanin ba, to al’ummomin dake zaune a jihohin Adamawa, Borno, Yobe, da kuma jahar Taraba su kwana da sanin daga karfe goma sha biyun na daren gobe za a dauke wuta har sai an biyasu hakkokinsu.

Yace sun fito zanga zangane saboda su nuna fushinsu dangane da irin zalunci da ake musu wanda acewar sa dole ne su nemi hakkinsu.

Shima anashi bangaren Jami’in kamfanin yace zasu tattauna da kungiyoyin domin ganin an shawo kan matsalar baki daya.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like