Ma’aikata Sunyi Zanga Zangar Rashin Samun Albashi A Yola


Da safiyar wannan laraban ne wasu ma’aikata sukayi zanga zangar rashin samun albashi har na tsawon watanni shida a Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa.

Ma’aikatan wadanda suka fara zanga zangar daga shatale-talen ‘yan sanda dake tsakiyar birnin Yola sun nufi gidan gwamnati daga bisani suka dangana da majalisar dokokin jihar.

Da yake yiwa gwamnan jihar wanda mataimakinsa Mr, Crowther Seth ya wakilta jawabi, jagoran masu zanga zangar Faisal Baba yace gwanmati bata kyauta musu ba, kasancewar ana biyan wasu albashi amma su kuma yau watanni shida kenan ba labari.

A wasikar da suka gabatar mata ma’aikatan sun bukaci gwamnati da dubi halinda suke ciki ta dawo da sunayensu cikin wadanda ake biya, ta kuma biyasu kudinsu na watanni shida da suka wuce.

Shima da yake maida martani ga ma’aikatan gwamnan ta bakin mataimakinsa yace babu ko shakka gwamnati tana sane halin da suke ciki kuma tana duba al’amarin, ba da dadewa ba za’a warware matsalar.

Jim kadan bayanda aka rantsar dashi a matsayin gwamna ne dai, gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya sanar da dakatar da duk wani ma’aikaci da aka dauka kafin ko kuma ranar 28 ga watan 9 na shekara 2019 wanda gwamna mai barin gado Mohammad Umar Jibrilla Bindow ya dauka.

©Zuma Times Hausa


Like it? Share with your friends!

-1
73 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like