Wannan sabuwar dokar ta zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Belarus ke ci gaba da murkushe zanga-zangar kalubalantar tazarcen Alexander Lukashenko, wanda ya haifar da dauri ko tilasta wa daruruwan ‘yan adawa da’ yan jarida yin gudun hijira.

Daga yanzu dai, duk wanda ya halarci zanga-zanga sama da biyu ba tare da izini ba, zai iya fuskantar hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari. Hakazalika an bullo da sabbin hukunce-hukunce don yakar “tsattsauran ra’ayi” ba tare da bayyana hakikanin fannin da ya shafa ba.

Sabuwar dokar ta Belarus ta tanadi daurin shekaru bakwai a gidan yari a kan duk wanda ya haddasa  “tashin hankali ko yin barazana ga ‘yan sanda, da kuma daurin shekaru uku ga duk wanda ya yi “turjiya” ga’ yan sanda.