Leah Sharibu Ta Haifawa Boko Haram Jariri


Wata majiya kusa da Boko Haram ta bayyana cewa, an tilastawa yarinyar nan ‘yar makarantar sakandiren Dapchi da taki barin addinin Kirista a hannun Boko Haram, yanzu ta karbi Musulunci har ma ta auri wani Kwamanda, kuma ta haifa masa jariri namiji.

Shekara guda kenan, da wani gungun mayakan Boko Haram ya yi garkuwa da Leah Sharibu da wasu abokan karatun ta mata, amma daga bisani su aka sake su, ita kuma aka cigaba da riketa a matsayin fursuna.

A cewar wani rahoto da Sahara Reporters suka wallafa an ce tilasta wa Leah Sharibu aka yi ta karbi addinin Musulunci, saboda an ki yarda a sake ta, saboda addinin ta.

Duk da kiraye kirayen da iyayenta, kungiyoyin addini da na sa kai, da kokarin da jami’an gwamnati da na tsaro suka ce suna yi na kubutar da ita, fiye da shekara guda kenan Leah Sharibu na tare da Boko Haram.

A ‘yan kwanakin baya bayan nan dai, Boko Haram sun bullo da wani sabon salo na kisan gilla, inda suke zabar wadanda suke ba Musulmi ba suna kashe wa, da sunan daukar fansa

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like