Layin Dogon Kano Zuwa Kaduna Zai Samar Da Guraban Aiki 20,000 – Ameachi
Ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi, ya ce akalla ma’’aikata 20,000 za a dauka a aiki idan an kamala aikin layin dogon da za a shimfida daga Kano zuwa Kaduna.

Ministan ya bayyana hakan ne a Kano yayin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da fara aikin shimfida layin dogon, wanda zai hade da inda na Kaduna ya tsaya.

Hakan na nufin idan an kammala, za a samu hanyar sufurin jirgin kasa tun daga Abuja har zuwa Kano.

A cewar Amaechi, ma’aikatan za su yi aiki tashoshi daban-daban, yana mai cewa hakan zai bunkasa tattalin arzikin yankin da zarar an kamala shi kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito ministan yana fada.

Ministan ya ce aikin ya kai tsawon kilomita 203 wanda zai kasance mai tagwayen layuka.

A ranar Alhamis shugaba Buhari ya kai ziyara Kanon, don kaddamar da wannan aiki da kuma wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta kamala.

Yayin ziyarar, Buhari ya je fadar mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.