Lauyoyi 120 Za Su Kare Wadanda Ake Zargi Da Kisan Janar Alkali


Sama da lauyoyi 120, ciki har da manyan lauyoyin Nijeriya masu matsayin SAN ne suka bayyana aniyarsu ta kare mutane 19 da aka kama da zargin kisan Janar Idris Alkali.

Lauyoyin sun bayyana aniyar tasu a ranar Laraba bayan da mutanen da ake zargin da aiwatar da kisan kan suka shigar da takardar neman beli ga Justice Daniel Longji na babbar kotun jihar Filato da ke Jos.

Lauyan wadanda ake zargin, Gyang Zi, ya gaya wa jaridar PUNCH cewar sun shigar da takardar neman belin biyo bayan gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu a kan laifuka biyun da duk sun musanta aikatawa.

Zi ya ce, “Sama da lauyoyi 120 suna so su shiga cikin tawagar lauyoyin da zasu kare wadanda ake zargin. Har yanzu ba a basu beli ba, amma an shigar da takardar neman belin. Wadanda ake zargin sun musanta aikata laifukan.”

Kakakin rundunar yan sandan jihar Filato, Matthias Tyopev, ya bayyana cewa an gurfanar da mutanen a kan laifin hada kai gurin aikata laifi da kuma kisan kai.

Ya ce, “Ana tuhumarsu da laifuka guda biyu – hada kai gurin aikata laifi wanda yake karkashin sashe na 97 da kuma laifin kisan kai karkashin sashe na 221 na kundin Shari’ar Arewacin Nijeriya ta Final Kod kamar yadda jihar Filato take amfani da ita. Gaba dayansu sun musanta aikata laifin. Yanzu an dage shari’ar zuwa 10 ga watan Disamba domin tattaunawa game da belin da suke nema. An cigaba da aje wadanda ake zargin a gidan yarin garin Jos.


Like it? Share with your friends!

2
127 shares, 2 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like