Laurent Gbagbo zai rabu da matarsa | Labarai | DWLaurent  Gbagbo ya ce bisa kin amincewa da yin rabuwa irin ta arziki, hakan tilasta masa shigar da takardar neman sakin matarsa a gaban wata kotu da ke birnin Abdijan. Masu ‘ya ‘ya biyu tun bayan daura masu aure a farkon shekarar 1989, ma’auratan sun shafe tsawon shekaru suna gwagwarmayar siyasa, kafin kama su a cikin watan Afrilun shekarar 2011 bisa zargin hannu cikin rikicin bayan zabe. A tsakiyar makon jiya an hango Laurent Gbagbo mai shekaru 76 a yayin da yake sauka filin jirgin saman Abdijan tare da wata tsohuwar ‘yar jarida budurwarsa Nady Bamba, bayan kotun ICC ta wanke sa daga zargin aikata laifukan yaki. To amma kuma sai dai ko baya ga budurwarsa, an ga mai dakinsa Simone Gbagbo mai shekaru 72, tana zantawa da shi, kan daga bisani ta yi wa wurin batan dabo.
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.