Lalong ya killace kansa bayan kwamishina ya kamu da cutar Korona


Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong da kuma sauran yan majalisar zartarwa ta jihar sun killace kansu bayan da kwamishinan ciniki da masana’antu,Abe Aku ya kamu da cutar Korona.

Dan Manjang, kwamishinan yada labarai na jihar shine ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

A cewarsa Lalong ya umarci sauran yan majalisar zartarwar jihar da su kai kansu a yi musu gwajin cutar Korona.

Ya ce bisa umarnin gwamnan za a kai gwajin yan majalisar zartarwar ya zuwa cibiyar binciken cututtukan dabbobi dake Vom.

Manjang ya kuma shawarci sauran jama’a da su guji kai wa kwamishinonin ziyara a lokacin da suka killace kansu.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like