Laifin aikata madigo yasa an kori wasu dalibai daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi


Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi dake garin Jega ta kori wasu dalibai mata su hudu da aka samu da laifin yin mad’igo.

Da yake tabbatarwa da yan jaridu faruwar lamarin, shugaban makarantar,Alhaji Aminu Dakingari ya ce jami’an tsaro da kuma masu aikin goge-goge da shara sune suka kama yan matan lokacin da suke tsaka da aikata laifin.

Biyu daga cikin yan matan da abin ya shafa sun fito ne daga garin Kontagora na jihar Neja daya daga birnin Kebbi dayar kuma daga jihar Sokoto.

Shugaban ya kara da cewa daliban sun gurfana a gaban kwamitin bincike da aka kafa inda suka amsa laifin da ake tuhumarsu da aikatawa.


Like it? Share with your friends!

-4
112 shares, -4 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like