Lai Muhammad:Muna da hujjar dake nuna yan adawa na yiwa gwamnati zagon kasa


Ministan yada labarai, Alhaji Lai Muhammad ya ce gwamnatin tarayya na da kwararan hujjoji kan shirin da yan adawa suke na yi wa gwamnatin zagon kasa.

Ministan ya fadi haka ne ranar Asabar a wurin taron lakcar azumin watan Ramadan karo na 12 da aka gudanar a Oro,jihar Kwara.

Ministan ya yi zargin cewa yan adawa na aiki tukuru wajen dumama yanayin siyasar da ake ciki ta hanyar hana gwamnati gudanar da mulki.

Ya ce hukumomin tsaro baza su kyale ko wane mutum ba ya dawo da hannun agogo baya kan irin nasarar da aka samu.

Muhammad ya kara da cewa jam’iyar PDP da kuma dantakarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar a zaben da ya gabata na yin duk mai yiyuwa wajen yiwa gwamnati zagon kasa.

You may also like