Labari Mai Dadi: An Gano Rigakafin Cutar Ƙanjamau


Bayan an kwashe shekaru 40 ana fafutkar neman rigakafin cutar nan mai karya garkuwar jiki (HIV/AIDS), wacce aka fi sani da Cutar Kanjamau da Hausa. Da alama dai hakan waɗannan masana ilimin kimiyya ya kai ga samun ruwa. Domin a jiya Daraktan bincike a cibiyar binciken kwayoyin cuta da kuma rigakafi mai suna Farfesa Dan Barouch shi ne ya shugabanci binciken.

Ya bayyana yadda wannan bincike da suka sa suna ‘HTVN 705’ ko ‘imbokodo’ Kuma a cewarsu, an dace da samun rigakafin ne bayan an gwada maganin a kan mutane da kuma birrai har aka dace. An yi wa mutane lafiyayyu guda 400 wannan rigakafi. Bayan wani lokaci kuma, aka ɗebi jininsu aka gwada. Sai aka samu jininsu na dauke da sinadarin da yake wa jikin ɗanadam garkuwa da cutar.

Su ma birran bayan an yi musu, an samu kashi 67% daga cikinsu sun samu garkuwa daga ciwon. Hakan dai ta kuma kasancewa bayan an gwada ta a kan matan kasar Afirka ta kudu guda 2,600. Ita dai wannan cuta ta kanjamau ta yi kaurin suna musamman da yake tana da haɗarin gaske, sannan ba a taɓa samun magani ko rigakafinta ba sai yanzu. Amma duk da haka ga har yanzu ba a samo maganinta ba a likitance ba.

Kuma bincike ya nuna cewa, kimanin mutane miliyan 37 ne suke rayuwa da cutar Kanjamau. Babban abin tsoron shi ne, a halin yanzu kowacce rana ba a gaza samun mutane Miliyan guda da dubu ɗari takwas da suka kamu da wannan cuta mai haɗarin gaske.


Like it? Share with your friends!

-1
141 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like