Labaran karya : EFCC ta gayyaci Fani Kayode da Odumakin


Hukumar EFCC mai yaki da yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta gayyaci tsohon ministan harkokin sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode da kuma Yinka Odumakin wani jigo a kungiyar Yarabawa ta Afenifere.

Mutanen sun rika yada labaran karya a kafafen sadarwar zamani inda suka ce hukumar ta EFCC ta kai samame gidan alkalin alkalan Najeriya, mai shari’a Walter Onnoghen.

Mai magana da yawun hukumar ta EFCC,Tony Orilade shine ya bayyana haka a wurin taron kungiyar masu wallafa jaridu ta kafar Intanet dake gudana a Abuja.

Orilade ya ce idan dukkanin mutanen biyu suka gaza bayar da bayanai masu muhimmanci to kuwa hukumar baza ta sake su akan lokaci ba.

Hukumar EFCC tace babu wani lokaci da ta kai irin wannan samamen gidan alkalin alkalan inda tayi barazanar daukar matakin shari’a.

Tuni Fani Kayode ya nemi afuwan hukumar kan karyar da ya sharara m sai dai ya dage cewa wata majiya mai tushe ta sheda masa cewa wasu mutane sun kai samame gidan Onnoghen sai dai bai san daga wace hukumar suka fito ba.

Ana sa bangaren Odumakin ya wallafa wani fefan bidiyo inda yace samamen da hukumar ta EFCC ta kai ne gidan alkalin alkalan.


Like it? Share with your friends!

-1
73 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like