Labarai A Takaice


– Ruwan sama kamar da bakin kwarya dauke da iska mai karfi sun yi sanadiyar hallaka mutane kusan 50 a Jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, yayin da gidaje sama da 200 suka rushe.

– A Najeriya hukumar Kula da Harkokin Kafafen Watsa Labarai ta kasar NBC ta gargadi daukan mataki nan ba da jimawaba kan kafofin da take bi bashin kudin da ya kai Naira biliyan 4.2.

– Rundunar Sojin Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa, dakarunta da motocinta sun bace bayan wani hari da kungiyar Boko Haram ta kaddamar mu su a garin Bama da ke jihar Borno.

– Kasa da sa’oi 24 bayan ziyarar da shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ya kai Najeriya, inda ya gana da shugaba Muhammadu Buhari kan dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma kisan da ake yiwa Yan Najeriya a kasar, an sake kashe wani dan Najeriya Martin Ebuzoeme.

– Rundunar ‘yan sandan India ta cafke maza 17 da ake zargi da yi wa wata karamar yarinya mai shekaru 11 fyade na tsawon makwanni, abin da ya tayar da hankulan al’ummar kasar.

– Ana ci gaba da sukar shugaban Amurka Donald Trump bayan ya kare Rasha daga zargin da ake yi ma ta na kutse a zaben shugabancin kasar da aka gudanar a shekarar 2016.

– Tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya fara ziyara a kasar Kenya inda zai kaddamar da wata Cibiyar horar da matasa. Da isar sa kasar a jiya, Obama ya gana da shugaba Uhuru Kenyatta da shugaban yan adawa Raila Odinga, kafin yau da safe ya tashi zuwa kauyen kakannin sa cikin matakan tsaro.

– Gwarzon dan wasan duniya, Christiano Ronaldo ya ce, yana godiya matuka da damar da kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta ba shi ta buga ma ta tamaula, lura da cewa, mafi tarin lokuta, ‘yan wasa masu yawan shekaru irin nasa na karewa ne a kungiyoyin kwallon kafa na Qatar ko China.

– Dan wasan Faransa, Kylian Mbappe da tauraruwarsa ke haskawa a duniyar tamaula zai yi sadaka da dukkanin kudaden da ya samu a gasar cin kofin duniya ta bana da aka kammala a Rasha da yawanssu ya kai kimanin Naira miliyan 160.


Like it? Share with your friends!

-3
34 shares, -3 points

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like