Labarai A Takaice


– Shugabannin jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya da jagororin wasu jami’iyyun 34, ciki har da sabuwar jam’iyyar R-APC da ta balle daga APC, sun taru a garin Abuja kan tunkarar zaben 2019.

– Gwamnatin Najeriya ta bayyana sauyin yanayi da wasu bata garin yan siyasa da kuma wadanda ke dawowa daga Libya a matsayin wadanda ke tinzira rikicin da ake samu tsakanin makiyaya da manoma. Gwamnatin tace yanzu haka tana da shaidun dake nuna mata wadannan gurbatattun yan siyasar.

– Wata kotu da ke yi wa ‘ya’yan kungiyar Boko Haram shari’a a Jamhuriyar Nijar ta yanke wa mutane 17 hukuncin daurin shekaru daban-daban saboda da samun su da hannu cikin ayyukan ta’addanci na kungiyar.

– Wani sabon rahoton Majalisar Dinkin Duniya na nuna matukar fargaba game da karancin kifaye a manyan teku na duniya duk da cewa mabukata cin-kifi da ke gina jiki na kara yawa. Rahoton na ganin kasashe masu tasowa na da gagarumin aiki don wadata kasashensu da wannan nau’in abinci.

– Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce nan da wani gajeren lokaci, gwamnatinsa za ta zaftare kudaden da ta ke kashewa wajen gudanar wasu muhimman ma’aikatun ta.

– An kubutar da daukacin yaran da suka makale a kogon Thailand.

– Hukumar kwallon kafa ta Spain ta bayyana tsohon kocin kungiyar Barcelona Luis Enrique a matsayin sabon mai horar da ‘yan wasan kasar.


Like it? Share with your friends!

2
35 shares, 2 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like