Labarai A Takaice


– A Najeriya gwamnonin yankin kudu maso gabashin kasar sun gudanar da wani taro a jihar Enugu a karshen mako, in da suka tsayar da shawarar hana zirga-zirgar shanu a yankin baki daya bisa fargabar hare-haren makiyaya.

– Amina Muhammad, mataimakiyar sakataren majalisar dinkin Duniya na ziyara a Jamhuriyar Nijar, inda a yau ta ziyarci Jihar Maradi don gani da ido, kan irin ayyukan da hukumomin Majalisar ke yi keyi kan hakkokin yara, ilimin mata, kiwon lafiya, da kananan sana’o’in mata sannan da batun canjin yanayi.

– Shugabannin Habasha da Eritrea sun sanya hannu kan yarjejeniyar sulhunta rikicin kan iyakar da ya lalata dangantakarsu a baya.

– Sakataren harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson ya yi murabus daga mukaminsa, matakin da ya zama babbar barazana ga gwamnatin Fira Ministan Birtaniya Theresa May, wadda ke fama da rarrabuwar kai dangane da shirin kasar na ficewa daga karkashin kungiyar kasashen turai EU.

– Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce nan da wani gajeren lokaci, gwamnatinsa za ta zaftare kudaden da ta ke kashewa wajen gudanar wasu muhimman ma’aikatun ta.

– Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya yi rantsuwar ci gaba da jagorantar kasar wa’adi na biyu, a karkashin wani sauyi na kundin tsarin mulkin da ya ba shi karin karfin fada-a-ji da kuma aiwatar da sauye-sauye kai tsaye.

– Firaministan Japan, Shinzo Abe ya soke ziyarar da ya shirya kaiwa kasashen ketare hudu bayan ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 100 a kasar.

– Jami’an agaji a Japan sun ce yawan wadanda suka hallaka a kasar sakamakon ambaliyar ruwan da ta aukawa yankunan yammaci da tsakiyar kasar ya karu daga 49 zuwa 60.

– Masu linkaya sun yi nasarar ceto shidda daga cikin dalibai shabiyu da malaminsu guda, da suka shafe fiye da makwanni 2 makale cikin wani kogo a arewacin kasar Thailand, sakamakon ambaliyar ruwan da ta mamaye hanyar shigarsa.


Like it? Share with your friends!

2
35 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like