Labarai A Takaice


– A Najeriya shugaban jam’iyyar APC mai mulkin kasar, Cif John Oyegun ya sanar da janye aniyarsa ta neman wa’adi na biyu na shugabancin jam’iyyar.

– Wasu ‘yan bindiga da ake zargin barayin shanu ne, sun kai hari a garin Zanuka, da yankin Bawar Daji, da ke jihar Zamfara, a inda suka hallaka mutane sama da 23.

– Hamshakin attajirin Najeriya ya taimakawa hukumar ‘yan sandan kasar da motoci 150 domin inganta tsaro, koda yake yayin da wasu ke yabawa wasu kuma na ganin da jami’an tsaron aka yiwa kyautar motocin.

– Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar rage shekarun tsayawa takarar zabe wadda za ta bai wa matasa damar shiga fagen siyasa domin damawa da su.

– Gwamnatin Kenya ta bayar da umurnin gudanar da bincike a kan wasu bankunan kasar 10 da ake zargi da boye kudaden da yawansu ya kai dala milyan 100 da wasu manyan jami’an hukumar aikin bautawa kasar suka kwashe.

– Gwamnatin Mali ta amince da fara aikin wata doka samar da zaman lafiya, ta zata bada damar yiwa ‘yan tawayen kasar Afuwa wadanda suka tada kayar baya a shekarar 2012, wanda ya basu damar kwace iko da yankin arewacin kasar a waccan lokaci.

– Gwamnatin Saudiya ta yi barazanar daukar matakin soji akan kasar Qatar, muddin ta sayi makamin kakkabo jiragen yaki ko makami mai linzami kirar S-400 daga Rasha.

– Faransa ta kaddamar da shirin bunkasa samar da sinadarin hydrogen domin bada damar fara amfani da shi a matsayin makamashi a masana’antu da kuma fannin sufuri.

– Hukumomi a Jamus sun ce an samu nasarar kamo zakuna biyu da damusa ukun da suka tsere daga gidan ajiye namun daji a wani yanki da ke yammacin kasar.

– Amurka ta ce a juma’a ta fara aiki da sabon tsarin biyan harajin karafa na 25% da kuma 10% na samfolo akan kasashen Turai da Canada da kuma Mexico.

– An sake zabar Guiseppe Conte a mukamin Firaministan kasar Italiya, wanda ya sanar da yi murabus ranar lahadi da ta gabata ,bayan da shugaban kasar ya nuna adawa dangane da sunayen wasu da aka gabatar masa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like