LABARAI A TAKAICE


HUKUMAR ZABE TA TSAIDA RANAR 16 GA WATAN NUWAMBA DON YIN ZABE A MAZABE SANATA DINO MELAYE A KOGI*
👇👇👇👇👇👇👇

*Hukumar zaben Najeriya INEC ta tsaida ranar 16 ga watan gobe ta zama ranar sake zabe a mazabar dan majalisar dattawa na Kogi ta yamma wato Sanata Dino Melaye. INEC ta dau matakin ne biyo bayan soke zaben Melaye da kotun karar zabe ta yi da hakan ya samu tabbatarwa a kotun daukaka kara.*

*Dan takarar APC Smart Adeyemi ya shigar da karar da ta kai ga soke zaben. Za a gudanar da zaben rana daya da zaben gwamnan jihar da za a gudanar a 16 ga watan na nuwamba. Kotu ta amince duk ‘yan takarar su sake shiga don gwada sa’ar su a zaben.*

*HUKUMOMI A KANO SUNCE ZAKI YA KOMA KEJIN SA CIKIN RUWAN SANYI*
👇👇👇👇👇👇👇

*Hukumomi a Kano sun ce bayan dogon artabu da aka sha, a karshe dai an samu rikakken zakin da ya tsere daga gidansa a gidan namun daji na jihar, ya koma dakinsa bayan an yi masu wasu ‘yan dabaru.*

*Shugaban hukumar gidan namun dajin ya ce bayan da allurar kashe jiki da aka yi masa ta ki yin aiki aka kuma kasa mayar da shi dakin nasa, sai aka yi masa dabara wajen daure akuya a cikin dakin inda bayan ya hangota, sai ya koma ciki.*

*”Akwai wani mai kula da shi da ke ba shi abinci mai suna Musbahu, wanda har yana iya magana da shi ta hanyar alamu, to da shi ne aka samu shawo kan zakin wajen nuna masa akuyar da aka ajiye a dakin nasa, hakan kuma ta sa nan da nan zakin ya shige ciki sai aka rufe,” in ji shugaban Gidan Zoo.*

*AN KASHE TIRILIYOYIN NAIRA KAN SAMAR DA WUTAR LANTARKI DAGA FARKON DIMOKRADIYYAR TA 1999 AMMA WUTAR BA TA ZAUNA BA*
👇👇👇👇👇👇👇

*Ba wani abun mamaki ba ne don an dauke wuta a Najeriya, amma abun mamaki ne wutar ta zauna a wuni ko sa’o’i a yawancin sassan Najeriya. Wutar dai hatta a daya daga manyan tashoshin wutar wato Kainji a jihar Neja ba ta wadatar da al’ummar yankin ba kuma hakan ma ba za a ce ya zama inuwar giginya ba da wasu jihohin a nesa kan samu.*

*Gwamnatin APC mai mulki a yanzu ta aza alhakin rashin ingancin wutar kan ta PDP da ta yi mulki tsawon shekaru 16. “daya daga tsoffin shugabanni a wancan karon har bugin kirji ya yi cewa ya kashe fiye da dala biliyan 15 kan samar da wutar, to ina wutar?….” Inji shugaba Buhari da ya ke nufin gwamnatin tsohon shugaba Obasanjo ta gaza samar da wutar duk da makudan kudin da ta kashe.*

*MAGOYA BAYAN MANYAN ‘YAN SIYASA A KANO SUN YI ARANGAMA HAR WASU SU KA SAMU RAUNUKA*
👇👇👇👇👇👇👇

*Magoya bayan manyan jam’iyyun siyasa ko ‘yan siysa wato ‘yan GANDUJIYYA sun yi arangama da ‘yan Kwankawasiyya inda mutum 8 su ka samu raunuka da kuma lalata motci 10. Lamarin ya auku ne lokacin da magoya bayan Kwankwasiyya ke dawowa daga Madobi wajen wani taron bude asibitin haihuwa da jagoran su Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gina.*

*PDP ta aza laifin kan APC inda APC ta yi watsi zargin.*

*SAKATAREN TSARON AMURKA MARK ESPER YA SAUKA A SAUDIYYA A TSAKIYAR TSAMIN DANGANTAKAR AMURKA DA IRAN*
👇👇👇👇👇👇👇

*Sakataren tsaron Amurka Mark Esper ya sauka a Saudiyya daidai lokacin da dangantakar Amurka da Iran ke tsami hakanan Rasha ke fadada angizon ta a yankin. Gabanin sauka a Saudiyya, Esper ya ziyarci Afghanistan. A na sa ran Esper zai samu ganawa da Sarki Salman da Yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman.*

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like