Labarai A Takaice


Yau Shugaban Kasa, Buhari Zai Gabatarwa Da Majalisar Kasa Kasafin Kudi Na 2020.

Kotun sauraron karar zaben gwamnan jihar Bauchi ta tabbatar da nasarar Bala Muhammad a matsayin gwamna.

Hukumar EFCC ta bukaci kotu ta kwace kaddarorin da Abdulrasheed Maina ya mallaka a gida da kasashen waje.

Shugaba Buhari ya sake mika sunan Adeshina don a sake zaben shugaban bankin raya Afrika.

Gamayyar kungiyoyin kwadago sun ce suna bukatar ganin sabon tsarin albashi ko kuma su shiga yajin aiki.

A jihar Bauchi kwalekwale ya kife da wasu manoma 40 a hanyarsu ta zuwa gona, 38 daga cikinsu sun rasu.

Akalla mambobi da magoya bayan jam’iyyar APC 6,000 ne suka koma PDP a jihar Bayelsa.

Kungiyar MURIC ta yi Allah wadai korar daliba daga makaranta saboda ta sanya Hijabi.

An kashe mutane 4 ta hanyar bude wuta a wata mashaya dake Amurka.

Zanga-zanga: Gwamnan Baghdad Babban Birnin Iraki Falah Al-Jaza’iri ya yi murabus.

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Turai, Michel Platini, ya kammala wa’adin dakatarwa da aka kakaba mai a harkar kwallon kafa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like