Labarai A Takaice


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tashi da tawagar da ta hada da gwamnoni zuwa birnin Newyork na Amurka don halartar babban taron majalisar dinkin duniya.*

*A yayin taron babbar majalisar, shugabannin duniya kan yi jawabi daya bayan daya kan lamuran da su ka shafi kasashen su da ke son kulawar majalisar.*

*Taron zai gudana karkashin sabon shugaban babban zauren Muhammad Bande wanda har ila yau shi ne wakilin Najeriya a majalisar.*

*Sashen Hausa na Muryar Amurka ya shirya taron tattaunawa ta musamman tsakanin wakilan kungiyoyin addinin musulunci da na kirista kan haramta kungiyar shi’a ta almajiran Ibrahim Elzazzaky da gwamnatin Najeriya ta yi.*

*Taron ya yi yunkurin tattaunawa don gano dalilan da kan sa muzaharar ‘yan shi’a kan ‘kare da fitina ko ma ta kai ga zubar da jini. Kazalika taron ya duba muhimmancin bin dokokin kasa da kaucewa fito na fito da jami’an tsaro kazalika da bin ka’idar fitowa zanga-zanga ga kungiyoyin da ke da wannan tsari.*

*Taron ya tabo zargin da a ke yi wa almajiran Elzazzaky na bin sawun juyin juya hali na Iran da kawo tsarin a Najeriya. Hakanan taron ya tabo batun auren nan na wucin gadi MUT’A da ‘yan shi’a su ka amince da yi inda ‘yan AHLUSSUNNAH ke zaiyana hakan da kulla huldar zinace-zinace ne.*

*Dr.Umar Labdo shi ya wakilci kungiyar JIBWIS a taron, yayin da Muhammad Ibrahim Gamawa ya zo a madadin almajiran Elzazzaky IMN. Babban sakataren ANSARUL TIJJANIYYA Alkassim Yawuri ya wakilci ‘yan Tijjaniyya da taimakon Murtadha Nuru Gusau.*

*Shi kuma Dr. Hafiz Sa’id Kano ya halarci taron daga cibiyar shi’a ta HAIDAR da ba ta bin muradun Elzazzaky a kungiyar IMN a takaice. PASTO Aminchi Abu da tsohon shugaban reshen matasa na kungiyar kiristoci ta Najeriya CAN Pastor Simon AS Dolly sun halarci taron a madadin mabiya addinin kirista.*

*Masanin harkokin siyasa Dr. Abubakar Kari da masanin tsaro Komred Aliyu Waziri ma sun halarci taron. CSP Sani Muhammad Baban inna ya zo taron a madadin rundunar ‘yan sandan Najeriya inda mai kare muradun mata Rahama Abdulmajid ta yi bayanai kan lamuran mata.*

*Ba a bar ‘yan kungiyar ma’abota kafafen labaru karkashin Buhari Yunusa Kumurya ba a taron da ya kai fiye da sa’a 3 kafin kammala a cibiyar muryar Amurka ta Abuja.*

*Karamin ministan wajen Saudiyya Adel Aljubeir Adel Aljubeir ya ce Iran ke da alhakin harin da a ka kai da jirage marar sa matuka kan kamfanin fetur din Saudiyya Aramco wanda shi ne mafi girma a duniya.*

*Aljubeir ya ce Saudiyya da kawayen ta na nazarin martanin da za su mayar kan harin da tun farko ‘yan tawayen Houthi da Iran ke marawa baya.:Ministan ya ce tuni an riga an gano makaman da a ka harba kirar Iran ne kuma an cillo su ne daga bangaren arewaci.*

*Shugaban kamfanin fetur na Saudiyya ARAMCO Amin Nassir ya ce kamfanin ya farfado daga harin da a ka kai ma sa kuma zai fara cikekken aiki zuwa karshen watan nan.*

*Harin kan cibiyar fetur ta Abqaiq da khuraish ya yi sanadiyyar tauye hako fetur na Saudiyya da rabi inda ya rage yawan fetur din da ganga miliyan 5.7 a wuni.*


Like it? Share with your friends!

1
33 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like