LABARAI A TAKAICE


Hukumar Alhazan Naijeriya (NAHCON) ta dawo da Adadin Alhazai dubu 34,002, cikin sawun jirage 70 zuwa gida Naijeriya bayan kammala Aikin Hajjin Bana.*

*Shugaban Zimbabwe na farko bayan ta sami ‘yancin kai Mista Robert Mugabe ya mutu yana da shekara 95. An hambarar da Mista Mugabe daga mulki ne a wani juyin mulki da aka yi masa a watan Nuwambar 2017, wanda ya kawo karshen mulkinsa na shekara 30.*

*An haife Mugabe ranar 21 ga watan Fabrairun 1924 a lokacin sunan kasar Rhodesia. Kuma an zabe shi a matsayin shugaban jam’iyyar ZANU 1973 a lokacin yana tsare a kurkuku. kuma yana cikin mutanen da suka kafa jam’iyyar.*

*Ministan wajen Najeriya Georfrey Onyeama ya ce daga yanzu Najeriya ta ja jan layi don kawo karshen hare-haren da ‘yan Afurka ta kudu ke kaiwa ‘yan Najeriya masu harkoki a kasar su. Onyeama na magana ne bayan ganawa da shugaba Buhari a fadar Aso Rock.*

*Ministan ya ce sam gwamnatin Najeriya ba za ta cigaba da lamuntar zaluntar ‘yan kasar ta a Afurka ta kudu ba. Duk da haka ministan ya ce ba gaskiya a labarin cewa wasu ‘yan Najeria sun rasa ran su a cin zarafin na Afurka ta kudu. Gwamnatin ta ce ta na magana da gwamnatin Afurka ta kudu don kawo karshen kalubalen.*

*Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Muhammad Adamu ya ba da umurnin tsaro mai tsaro a dukkan ofisoshin jakadanci da kuma sassan kasuwancin ‘yan ketare a Najeriya. Wannan ya biyo bayan hare-haren ramuwar gaiya da wasu ‘yan Najeriya su ka yi kan kadarorin Afurka ta kudu.*

*Tuni ma randunar ta ce ta kama wadanda a ke tuhuma da kai hari kan kadodorin na Afurka ta kudu mutum 125. Kazalika rundunar ta ce ta kwato wasu daga kayan da mutanen su ka yi warwaso a tunzurin nuna fushin su ga kashe ‘yan kasuwar Najeriya a Afurka ta kudu.*

*Rundunar ta ce mutanen na da damar nuna fushin su kan abun da ya yi mu su zafi, amma hakan ya zama wajibi ya zama ta hanyar da doka ta amince da ita.*

*Kungiyar kwadago ta kamfanoni masu zaman kan su TUC ta nuna matukar damuwa ga yadda ‘yan Afurka ta kudu ta farwa ‘yan Najeriya da cin zarafi har ma da kisa, duk da yadda Najeriya ta taimaki Afurka ta kudu ta samu ‘yanci daga wariyar launin fata.*

*Jami’in kungiyar Nuhu Toro ya yi karin bayani bayan sanarwa da kungiyar ta rabawa manema labaru. Toro ya ce akwai lokacin da ta kai ga ma’aikatan Najeriya su ka tara gudunmawa su ka aikawa kungiyar gwagwarmayar bakaken fata ANC karkashin marigayi Nelson Mandela.*

*TUC ta bukaci shugaban Afurka ta kudu Cyril Ramaphosa ya dau matakan hana bata gari kai hari kan ‘yan Najeriya da al’ummar wasu kasashen da ke zaune a kasar. Duk da haka, TUC ta ce ba daidai ba ne huce haushi da wasu matasan Najeriya su ka yi kan kamfanin sadarwa na NTN da kasuwar SHOPRITE duk mallakar ‘yan Afurka ta kudu a manyan biranen Najeriya.*

*Jami’ar kare hakkin dan Adam ta majalisar dinkin duniya Michelle Bachelet ta ce fiye da farar hula 1000 su ka rasa ran su a kasar Sham cikin wata 4 da su ka gabata.*

*Cikin mutanen har da yara 304. Akasarin wadanda su ka mutu sun rasa ran su ne sakamakon ruwan boma-bomai ta jiragen yaki da gwamnatin Damaskas ta Bashar Al-Asad ta jagoranta. Bachelet ta ce yara ma na cikin zullumin rasa ilimi a yankin arewa maso yammacin Sham da a ka yi wa rugu-rugu da hakan ya jawo rufe makarantu.*


Like it? Share with your friends!

-1
35 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like