LABARAI A TAKAICE


Gwamnoni daga jihohin Najeriya 36 sun yi taro da shugaba Buhari a fadar Aso Rock kan kalubalen tsaro da ke addabar wasu sassan Najeriya musamman arewa maso yamma da arewa maso gabas da kuma satar mutane da ya ta’azzara.*

*Hafsoshin rundunonin tsaro ma sun halarci taron da kazalika ya samu halartar tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul’azizi Yari Abubakar.*

*Daga bisani an fahimci taron bai cimma matsaya kan bukatar kafa ‘yan sanda mallakar jihohi ba da dama batun ke haddasa muhawara cewa gwamnoni za su iya amfani da su tamkar ‘yan bangar siyasa. An ga sabbin fuskoki a gwamnonin da a ka rantsar kwanan nan a taron a sakamakon zabe a jihohi 29 cikin 36. An ga sabon gwamnan Bauchi Bala Muhammad, na Borno Babagana Umara Zullum, na Gombe Inuwa Yahaya da sauran su.*

*Gwamnonin sun yi raha da juna da ya nuna taron ya zama bigiren yin sabbin abokai ko kulla dangantakar gwamnoni ba tare da bambancin jam’iyya ba.*

*Babbar kotun taraiya ta Abuja ta yanke hukuncin a damkawa tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha shaidar lashe zaben majalisar dattawa daga jihar bayan janye ba da takardar sakamakon shaidar cewa wanda ya ba da sanarwar ya ce an tilasta shi ne ya ambata Rochas a matsayin wanda ya lashe zaben.*

*Jostis Abang Okong na babbar kotun ya ce hukumar zabe ba ta da ikon hana ba da takardar bayan an sanar da wanda ya lashe zabe. Okorocha ya nuna farin ciki da sakamakon hukuncin. Yanzu dai ba a san ko akwai daukaka kara kan lamarin ba ko za a samu rantsar da Okorocha a majalisa ta 9 da za ta fara aiki ranar talata mai zuwa.*

*Babbar kotun taraiya ta umurci hukumar kula da kafafen sadarwar Najeriya NBC ta dakatar da rufe gidan talabijin na AIT har sai an kammala sauraron karar da kamfanin ya shigar. NBC dai ta janye lasisin gidan talabijin din sakamakon samun sa da saba dokokin sadarwa daga shirin sa na siyasa KAKAAKI.*

*Yanzu dai za a baiyana gaban kotun ranar 13 ga watan nan don fara sauraron karar. Lauyan kamfanin Mike Ezekhome ya samu takardar umurnin kotun don neman jin bahasin kamfanin kafin yanke hukunci bisa tanadin doka.*

*‘Yan adawa a Sudan sun amince da shiga tsakani na Firaministan Habasha Abiy Ahmed kan takaddamar su da gwamnatin sojan kasar da ta kawar da gwamnatin Omar Elbashir. Duk da haka ‘yan adawan sun kafa sharadin sojojin su dau alhakin kashe ‘yan zanga-zanga da kuma barin masu bincike na duniya masu zaman kan su, su shigo lamarin.*

*Abiy Ahmed ya bukaci dawo da mulki hannun farar hula ba da bata lokaci ba.*

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like