LABARAI A TAKAICE


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya buakci daukar matakai wajen hana shigowar makamai Najeriya da ke kasashen yankin Sahara da su ka hada har da kasar Libya da ke cikin fitinar ‘yan bindiga tun kisan gilla ga shugaba Moammar Ghaddafi a 2011.*

*Shugaba Buhari na magana ne a taron kasashen yankin Sahara a birnin Ndjamena na Chadi karkashin jagorancin shugaba Idris Derby. Ga illar barin kananan makamai na shigowa daga yankin cikin Najeriya, shugaban ya bukaci daukar matakan hana cigaban hakan don dakile isar makaman hannun miyagun iri.*

*A sanarwa daga mai taimakawa shugaban kan labaru Garba Shehu, ta ce shugaban zai kawo batun fataucin mutane a yankin da ke cikin wannan illar ta kalubalen tsaro. Aikin kasashen yankin da na tafkin Chadi na da muhimmancin gaske wajen ragewa ko ma karya alkadarin ‘yan ta’adda na kasa da kasa.*

*Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnati na da kwarin guiwa wajen ceto yarinyar nan daya da ta saura a hannun ‘yan Boko Haram Leah Sharibu. Yarinyar dai na daga cikin matan makarantar Dapchi a jihar Yobe da ‘yan Boko Haram su ka sace amma daga bisani su ka dawo da dukkan matan amma su ka sake tafiya da Sharibu da fakewa da cewa ta ki barin addinin kirista ne ya sanya hakan.*

*Shugaban ya ce an samu nasarar magana da ‘yan ta’addan da ke rike da yarinyar inda su ke nuna fargabar yawan jami’an tsaro a yankin da a da su ke cin Karen su ba babbaka, yanzu zai yi wuya su iya bugun kirjin dawo da Leah don tsoron rayuwar su. Duk da haka shugaban ya ce akwai kyakkyawar fatar samun Leah ya koma hannun iyayen ta.*

*Game da sauran matan Chibok kuma, Shugaba Buhari ya ce gwamnati ba ta mance da sauran matan ba ya na mai nuna farin cikin gwamnatin sa ta samu nasarar ceto mata 107.*

*An yi jana’izar Galadiman Katsina kuma hakimin MALUMFASHI a jihar Katsina a Najeriya, Jostis Mamman Nasir wanda ya rasu bayan fama da jinya. Danejin Katsina hakimin Mahuta ne ya jagoranci sallar jana’izar da ta samu halartar Sarki da mataimakin gwamnan Katsina don gwamna Aminu Bello Masari ba ya gari.*

*Marigayin dai ya shahara a banagaren shari’a a Najeriya inda a ka radawa wani titi a anguwar Asokoro Abuja sunan marigayin. Kwanakin baya masu satar mutane sun yi yunkurin sace marigayin inda Allah ya kubutar da shi. Ba shakka za a rika tuna marigayin a sahun manyan dattawan arewacin Najeriya.*

*Allah Ya yiwa Modibbo Hafsatu Maigandi Mahaifiyar shaharraren malamin addinin Musulunci a Naijeriya Shiekh Dr Mansur Sokoto rasuwa. Modibbo ta rasu jiya Asabar a asibitin UDUTH dake garin Sokoto. Za ayi jana’izarta yau Lahadi da misalin karfe takwas na safe a masallacin shehu a Unguwar Digar Agyere a birnin sokoto*

*Biyo bayan murabus din Bin Auwf a matsayin shugaban rikwan kwarya na soja a Sudan, yanzu mai rike da kujerar Abdelfatah Burhan Abdelrahman ya janye dokar hana yawon dare da alwashin yin shari’a ga wadanda su ka muzgunawa masu zanga-zangar da ta kai ga kawar da gwamnatin Omar Elbashir.*

*Abdelrahman wanda shi ne na uku mafi girman mukami a sojan kasar, ya tabbatar da komawa mulkin farar hula bayan shekaru biyu. Masu zanga-zanga sun yi shagali don murabus din Bin Auwf da su ke dauka na hannun daman tsohon shugaba Elbashir ne.*

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like