LABARAI A TAKAICE


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna muhimmancin shugabannin addini ga bunkasa zaman lafiya da hadin kan kasa. Shugaban wanda sakataren gwamnati Boss Mustapha ya wakilta, ya baiyana haka ne a fadar Aso Rock lokacin da ya ke ganawa da shugabannin addinin musulunci da na kirista.*

*Malaman sun yi addu’ar gudanar da zaben ranar asabar lafiya inda akasarin su, su ka ce ba wa shugaba Buhari dama ya ci gaba da mulki shi ne mafi a’ala.*

*Sheikh Kabiru Haruna Gombe na daga wadanda su ka halarci ganawar daga kungiyar JIBWIS inda wasu manyan ‘yan darikar Tijjaniya ke tambayar sa gaskiyar labarin wai ya ce kuri’un ‘yan Izala kadai sun isa dawo da Buhari kan mulki don haka ba ya bukatar na ‘yan darika. Sheikh Gombe ya yi watsi da labarin da nuna bai taba ambatar wani abu mai kama da wannan ba.*

*Sakataren Jam’iyyatul Ansarul Tijjaniya Alkassim Yawuri na cikin wadanda su ka bukaci gaskiyar wannan labarin.*

*Mabiya addinin kirista daga majami’ar Methodist da sauran matasan kirista na arewa sun halarci taron da fatar alheri ga Najeriya.*

*Dan takarar jam’iyyar APC shugaba Muhammadu Buhari ya kammala rangadin kamfen din sa da gudanar da gangami a Abuja. Shugaban Buhari wanda ya samu zagayawa dukkan jihohin Najeriya don neman wa’adi na biyu na mulkin sa bayan wannan wa’adi ya kammala a ranar 29 ga watan mayu.*

*PDP a na ta bangare ta yi zargin an hana ta filin gudanar da kamfen din karshe don haka ta janye yin hakan a Abuja. Hukumar zabe ta ci gaba da ba da tabbacin gudanar da zabe mai adalci da bukatar dukkan ‘yan kasa su fito don zaben wanda su ke so.*

*Manyan ‘yan takarar shugabancin Najeiya a ranar asabar din nan 16 ga watan nan na Febreru sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a mataki na karshe. Taron sanya hannun ya samu halartar masu ruwa da tsaki na ciki da wajen Najeiya.*

*Harin bom na kunar bakin wake ya yi sanadiyyar mutuwar akalla jami’an tsaron cikin gida na musamman na Iran inda wasu mutum 20 su ka samu raunuka. Harin ya auku ne a yankin Sistan da Baluchistan. Hukumomin Iran sun aza laifin bisa kungiyar ‘yan Alka’ida.*


Like it? Share with your friends!

-1
36 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like