Labarai A Takaice


Shugaba Buhari yayin jawabin sa a Zamfara, ya roki Allah samun damina mai albarka domin a samu abinci in yaso duk rigimar da za a yi sai ayi tayi.

Wani matashi, mai suna Kabir Matazu ya yi alkawarin kashe kan sa idan Buhari ya fadi zaben da za a yi ƙarshen mako.

Mutane 3 ne suka mutu wasu da dama sun suma saboda turmutsutsun jamaa yayin yakin neman zaben Atiku a jihar Kano.

Sojoji sun fara farautar masu garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Sheikh Ahmad Gumi ya yi kiran cewa ka da a siyasantar da kungiyar Izalah.

Gwamna Ganduje ya yaye sabbin dakarun Karota da aka horas, inda ya horesu da yin aiki tuƙuru.

‘Ta tabbata APC ba ta da ‘yan takara a jihar Zamfara domin Buhari bai daga hannun kowa ba’ Rahoto.

Sanata Ubale Shitu na jihar Jigawa ya ce duk wanda ya zabe shi ya kuma zaɓi Buhari bai yafe ba.

Wani matashi Yahaya Ahmad Usman daga jihar Taraba ya ƙera jirgin sama.

An yi arangama tsakanin magoya bayan APC da PDP a jihar Gombe.

An kama bakin haure ‘yan kasar Afganistan su 62 a Turkiyya.

Ebola ta kashe mutane 502 cikin watanni shida a Kongo.

EPL: Manchester City ta ci Chelsea 6:0 a wasan jiya.

Seria A: Juventus ta ci Sassoulo 3:0 a wasan jiya.

LaLiga: Barcelona da Athletic Bilbao sun tashi 0:0 a wasan jiya.

Wane Labari ne Yafi jan Hankalin ka/Ki


Like it? Share with your friends!

1
39 shares, 1 point

Comments 1

Your email address will not be published.

  1. Gaskiya banyarda buhari zaifadi hakaba yaroki damana mai albarka amma kuma yace duk rigirmarda za’ayi ayi haba jama’a arinka adalci acikin zance

You may also like