Labarai A Takaice


Kungiyar tarayyar Turai masu sanya ido a kan zabe sun ce kalaman El-Rufa’i ba zai sa su janye sanya idanu akan zaɓe ba.

Wasu matasa a jihar Benuwe sun kona tsintsiya tare da wanke filin da Buhari ya yi taron kamfen.

Dan takarar mataimakin shugaban kasa, Mr Peter Obi ya ce Najeriya za ta ruguje idan aka sake zaben Buhari.

Hukumar EFCC ta kama wasu matasa ‘yan damfarar yanar gizo su 11.

Gwamnatin jihar Kano ta bai wa Atiku Abubakar filin wasa na Sani Abacha don ya gudanar da taron siyasa a wurin.

Jam’iyyar PDP ta dakatar da yakin neman zabenta a jihar Zamfara saboda kashe-kashen da ake yi.

Rundunar sojin sama ta samu karin jiragen yaki 22 domin yakar ta’addanci a Najeriya.

Sufeto janar na ‘yansanda ya sauya kwamishinonin ‘yansandan jihohi, ciki har da na Kano.

Sanata Shehu Sani ya ce wadanda suka taya Atiku gwanjon kadarorin kasar a baya su ne ke tare da shugaba Buhari a yanzu.

Hukumar EFCC ta damke tsohon shugaban NIA, Oke da matarsa.

Hukumar Lafiya da Duniya (WHO) ta fitar da gargadi dangane da kai wa jami’anta hari a kasar Libiya.

EPL: Manchester City ta ci Everton 2:0 a wasan da suka buga jiya.

Spain Copa del Ray: Barcelona da Real Madrid sun tashi 1:1 a wasan da suka buga jiya.


Like it? Share with your friends!

-2
40 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like