Kwastam sun kwace mota dauke da shinkafar ƙasar waje buhu 300 a jihar Niger


Hukumar Kwastam ta Najeriya dake kula da yankin jihar Niger, ta kama wata babbar mota dauke da shinkafar ƙasar waje buhu 300 da darajarta ta kai naira miliyan ₦5.1 akan hanyar Kontagora.

Mista Benjamin Binga, kwantirola me kula da jihohin Niger, Kwara da Kogi shine ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN haka a Minna, ranar Alhamis.

Ya ce ma’aikatan hukumar dake aikin sintiri sune suka kama motar dake da rijistar namba SUL 616 XA an cikata da haramtattun kayan.

Kwantirolan ya shawarci masu fasa kwaurin kaya da su guji aikata haka, suzo su rungumi tsarin gwamnatin tarayya kan harkar noma wanda ke da burin bunƙasa tattalin arzikin kasa.

“Gwamantin tarayya nason karfafa shirin samar da shinkafar gida saboda mu zama masu dogaro da kai da kuma tattalin asusun musayan kuɗaɗen  ƙasar waje.

“Rundunar za ta cigaba da kare kan iyakoki da kuma dakile aiyukan masu fasa kwauri. Babu wurin buya ga masu fasa kauri a wannan yankin tun da duk haramtattun  hanyoyin da suke bi an gano su kana aka toshe su,”yace.

Kwantirolan ya kuma yi kira ga shugabannin al’umma da kuma masu rike da sarautun gargajiya musamman mazauna garuruwan kan iyaka su taimakawa gwamnati a kokarin da take na hana fasa kauri a kasarnan.


Like it? Share with your friends!

-1

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like