Kwankwaso ya yi barazanar ficewa daga PDP


Toshon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi barazanar ficewa daga jam’iyar PDP matuƙar shugabancin jam’iyar na kasa ya cire yan kwankwasiya daga jerin sunayen mutanen da za su tsayawa jam’iyar takara.

Idan za iya tunawa tsagin kwankwaso na jam’iyar PDP ya gudanar da zaben fidda gwani inda aka tsayar da magoya bayansa a matsayin yan takara ba tare da la’akari da sauran yan takarkarun ba.

Toshon gwamnan ya yi wannan gargadin ne a wurin taron sulhu da ake gudanarwa a birnin tarayya Abuja.

Taron wanda aka gudanar jiya ya samu halartar sanata Bello Hayatu Gwarzo, Ambasada Aminu Wali da kuma sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyar PDP reshen jihar Kano.

An gudanar da taron ne domin duba jerin sunayen yan takara da aka tsayar a jihar.

An dai tashi daga taron ba tare da cimma matsaya ba duk da tsoma bakin dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyar PDP, Atiku Abubakar ya yi.


Like it? Share with your friends!

1
60 shares, 1 point

Comments 5

Your email address will not be published.

  1. Write a comment *Agaskiya baikamata ayiwa Salihu Sagir Takai ba irin butulcin ba domin ya rike alkawari kuma bai bi Maigidan saba .

You may also like