Fadar gwamnatin Najeriya ta mayar da martani, dangane da kiran da fitaccen malamin addinin Katolika Rev. Fr Ejike Mbaka ya yi na cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka a mulki ko a tsige shi.

Cikin wata sanarwa da fadar ta fitar dauke da sa hannun kakakin Buhari Malam Garba Shehua ranar Juma’a, fadar ta ce kwangila malamin addinin ya nema aka hana shi, dalilin kenan da ya sa ya sauya goyon bayan da yake nunawa Buhari.

A ranar Laraba, Rev. Mbaka ya soki yadda gwamnatin Buhari take tafiyar da sha’anin tsaro a kasar, yana mai cewa ta gaza wajen kare rayukan al’umar kasar.

Muna tafe da karin bayani……