Kwamitin Wanzar Da Zaman Lafiya A Tsakanin ‘Yan Najeriya Ya Gudanar Da Wani Taro A MinnaKwamitin wanzar da zaman lafiya a tsakanin ‘yan Najeriya da tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya, Janar Abdussalam Abubakar, ke shugabanta ya gudanar da wani taro a Minna, fadar Gwamnatin Jihar Neja.

NIGER, NIGERIA – Manufar taron dai shi ne tabbatar da ganin ‘yan siyasa sun gudanar da yakin neman zaben shekara mai zuwa a kasar cikin lumana ba tare da samun wata matsala ba.

Tsohon shugaban Najeriya Janar Abdussalam Abubakar ya ce sun gudanar da taron ne domin shirya fadakar da ‘yan Najeriya akan sanin ‘yancinsu a lokacin zaben, da kuma nuna bukatar ganin ‘yan siyasa sun yi yakin neman zabe cikin lumana.

Kwamitin Wanzar Da Zaman Lafiya A Tsakanin ‘Yan Najeriya Ya Gudanar Da Wani Taro A Minna

Kwamitin Wanzar Da Zaman Lafiya A Tsakanin ‘Yan Najeriya Ya Gudanar Da Wani Taro A Minna

Shugaban hukumar zabe ta Najeriya farfesa Mahmod Yakubu yana cikin mahalarta taro ya kuma bada tabbacin kara inganta al’amuran zaben.

Mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya Sultan Sa’adu Abubakar da Rabaran Mathieu Hassan Kuka, da Alhaji Aliko Dangotte na cikin mahalarta taron. Sai kuma Janar Matuluta Agwai wanda ya bayyana muhimmancin taron a adai-dai wannan lokaci da babban zabe ke kawo jiki.

Kwamitin dai ya ce a ranar 29 ga wannan wata na Satumba zai gudanar da taron sanya hannu a yarjejeniyar yin yakin neman zabe lafiya a tsakanin ‘yan siyasa a kasar.

Saurari cikakken rahoton daga Mustapha Nasiru Batsari:


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg