Kwamitin Majalisar Wakilai Ya Saurari Ra’ayoyin Jama’ar Kano
Batun kara yawan alkalan kotun kolin Najeriya da fadada hurumin kotun daukaka kara da kirkiro sabbin jihohi da baiwa kananan hukumomin ‘yanci na hakika da kuma shigar sarakunan gargajiya wajen tafiyar da horkokin mulki, su ne batutuwan da aka tattauna da Kwamitin Majalisar Wakilan Najeriya a jihar Kano.

Wakilan kungiyar kwadagon Najeriya da na ‘yan gwagwarmayar shugabanci na gari da shugabannin al’uma da malaman addini da lauyoyi da kuma sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki daga jihohin Katsina da Kaduna da Kano da kuma Jigawa ne suka halarci taron jin ra’ayin.

Dakta Kamal Abdulkadir Mustafa, Talban Gaya shine ya gabatar da kasidar nanata bukatar kirkrio sabuwar jihar Tiga daga jihar Kano ta yanzu, yunkurin da ya ce sun fara tun fiye da shekaru 30 baya.

A karo na uku, su ma ‘yan kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta Najeriya NULGE, sun jaddada bukatarsu ta neman baiwa kananan hukumomin Najeriya 774 cikakken ‘yanci, kodayake sun dade suna zargin gwamnoni da yiwa wannan yunkurin nasu kafar ungulu.

Hon. Alhassan Ado Doguwa wadda shine ya jagoranci zaman kwamitin a Kano, ya ce babu ko shakka ra’ayoyin da jama’a suka bayyana ga Majalisar za ta yi aiki dasu.

A makon jiya ne dai, itama Majalisar Dattawan Najeriya ta yi makamancin wannan taro a jihar Kaduna.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg