Kwamishinoni uku sun kamu da cutar Korona


Mutane uku daga cikin yan majalisar zartarwar jihar Oyo sun kamu da cutar Korona.

Gwamnan jihar, Seyi Makinde shi ne ya bayyana haka cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Cikin sakon gwamnan ya ce sun samu sakamakon gwajin cutar Korona na yan majalisar zartarwa ta jihar inda aka samu uku daga ciki na dauke da cutar yayin da ake dakon sakamakon mutane biyu.

Jihar Oyo na da mutane 1,055 da suka kamu da cutar.

Shi ma gwamnan jihar ya kamu da cutar a watanni baya amma ya warke bayan da ya shafe mako guda yana jiya.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like