Kwamishinan zaben Imo ya bada umarnin kama jami’in tattara sakamako da ya sauya alkaluman zabe


Francis Otunta, jami’in tattara sakamakon gwamna a jihar Imo ya bayar da umarnin kama Kelechi Thankgod jami’in tattara sakamako na karamar hukumar Ohaji Egbema wanda aka zarga da sauya alkaluman sakamakon zaben karamar hukumar.

Otunta wanda yace yana da sakamakon zaɓen da aka tattara daga akwatuna ya bayyana cewa an sauya sakamakon da Thankgod ya kawo.

Ya zuwa yanzu a sakamakon da aka tattara,Emeka Ihedioha dantakarar jam’iyar PDP shine ke kan gaba.


Like it? Share with your friends!

-3
111 shares, -3 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like