Kwamishinan lafiya na jihar Benue ya mutu


Kwamishinan lafiya na jihar Benue, Emmanuel Ikwulono ya rasu.

A cikin watan Agusta ne kwamshinan ya karbi rantsuwar kama aiki kasa da watanni uku kenan.

Gwamnan jihar, Samuel Ortom ya maye gurbinsa da Dr Sunday Ongbabo wanda a kwanakin baya yayi murabus daga majalisar zartarwar jihar.

Ikwulono ya mutu ne a wani asibiti dake jihar Filato inda ya je ayi masa aikin tiyata kan wata cuta da take damunsa da ba a bayyana ba, kamar yadda gidan rediyon gwamnatin tarayya na Harvest Fm dake Makurdi ya bayyana.

Wasu majiyoyi dake gidan gwamnatin jihar sun bayyana cewa kwamshinan ya mutu ne sanadiyar sarkakiya da aka samu lokacin aikin tiyatar da aka yi masa.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 1

You may also like