Kwamishina da sakataren gwamnati sun kamu da cutar KoronaSakataren gwamnatin jihar Delta,Chiedu Ebie

Sakataren gwamnatin jihar Delta,Chiedu Ebie da kuma kwamishinan yada labarai na jihar, Charles Aniagu sun kamu da cutar Korona.

Mista Olisa Ifeajika, sakataren yada labaran gwamnan jihar, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Asaba babban birnin jihar.

Ifeajika ya ce dukkanin mutanen biyu sun nuna alamun cutar abin da yasa suka kai kansu aka yi musu gwaji.

Ya ce an kai dukkanin mutanen cibiyoyin killace masu dauke da cutar dake jihar kuma suna murmurewa.

Sakataren yada labaran ya shawarci mutanen jihar da su cigaba da bin dukkanin ka’idodin kare kai daga kamuwa da cutar saboda kowane mutum zai iya kamuwa da cutar komai matsayinsa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like