Kwamishina a jihar Lagos ya fice daga jam’iyar APC


Wale Oluwo, kwamishinan makamashi da muadanai na jihar Lagos,ya fice daga jam’iyar APC inda ya ci alwashin goyon bayan Jimi Agbaje dan takarar gwamnan jihar a jam’iyar PDP.

Wata majiya a jam’iyar PDP ta fadawa jaridar The Cable cewa Oluwo ya tuntubi ɓangaren Agbaje gabanin zaben 2019.

Fusataccen dan jam’iyar ya kuma fita daga gwamnatin Akinwumi Ambode.

A takardar sa ta barin aiki da jaridar The Cable ta gani,Oluwo ya zargi shugabancin jam’iyyar na jihar da yin watsi da tanade-tanaden dimakwaradiya a tsarin da suka bi na fitar da Babajide Sanwo-Olu a matsayin dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyar.

Sanwo-Olu shine mutumin da ya kayar da gwamnan jihar, Akinwumi Ambode a tsaben fidda gwanin dantakarar gwamna a jam’iyar ta APC.


Like it? Share with your friends!

-1
96 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like