Kwamandan kungiyar Boko Haram ya fada hannun jami’an tsaro


Sojoji dake aikin tabbatar da tsaro a yankin arewa maso gabas sun kama,Maje Lawal wani kwamanda a kungiyar Boko Haram da ake nemansa ruwa a jallo.

Maje ya fada hannun jami’an soja a garin Banki dake jihar Borno.

Mutumin da ake zargi na daga cikin jerin sunayen kwamandodin kungiyar ta Boko Haram da jami’an tsaro suke nema kuma sunasa ne na 96 a jerin sunayen.

A wata sanarwa mai dauke da sahannun Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojan Najeriya, Birgediya Janar Texas Chukwu, ya bayyana cewa an kama mutumin ne lokacin da ya shiga sansanin yan gudun hijira dake yankin.

Janaral Chukwu an yiwa mutumin da ake zargi binciken farko kana a mika shi hannun hukumomin da suka dace domin daukar mataki na gaba.


Like it? Share with your friends!

-2
75 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like