Kungiyoyin yakin neman zaben Buhari 59 sun koma goyon bayan Atiku


Wasu kungiyoyi 59 dake wa shugaban kasa Muhammad Buhari yakin neman zabe sun koma goyon bayan Atiku Abubakar.

Atiku wanda shine dantakarar shugaban kasa a jam’iyar adawa ta PDP da ake ganinsa a matsayin babban mai kalubalantar shugaban kasa Muhammad Buhari.

A wani taron manema labarai da suka gudanar a Abuja, kungiyoyin sun bayyana cewa sun yanke shawarar goyon bayan Atiku ne sakamakon gazawar da gwamnati mai ci ta yi.

Yusuf Ardo jami’in tsare-tsare na kasa a kungiyar Grassroots Mobilisers for Buhari (GMB)ya zargin gwamnatin Buhari da kin bawa matasa mukamai.

Ya ce kungiyar na da mambobi sama da miliyan biyar da suka karade ko wane yanki na kasarnan a yakin neman zaben Buhari a shekarar 2015.

Ardo ya kara da cewa tun bayan hawan gwamnatin yawan marasa aikin yi ke kara karuwa.

Ya kuma ce suna da tabbacin cewa Atiku zai farfado da tattalin arzikin kasarnan dake cikin mawuyacin hali.

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like