Kungiyar ‘Yan Jarida a Najeriya (NUJ) Ta Gargadi Mambobinta Da Su Guji Saba Ka’idar Aiki
Kaduna, Nigeria – Kafafen yada labarai dai kan taka rawa wajen yada manufofin ‘yan takarar kujerun siyasa da jam’iyyunsu a lokacin yakin neman zabe, sai dai kungiyar ‘yan jarida reshen jihar Kaduna ta ce wajibi ne ‘ya’yan kungiyar su bi ka’idojin aikin jarida wajen yada manufofin ‘yan takara da jam’iyyu.

Hajiya Asma’u Halliru Yawo, ita ce shugabar kungiyar ‘yan jarida ta NUJ a jihar Kaduna wacce kuma ta jagoranci shirya taron bitar, ta ce sun shirya taron ne saboda ya kamata a ja kunnen ‘yan jarida akan su guji bin ‘yan siyasa tunda su ba ‘yan siyasa ba ne, kuma a matsayinsu na shugabanni zasu horar da duk dan jaridar kungiyar da ya saba ka’idar aiki.

Tsohon mai magana da yawun gwamnan jihar Kaduna Alhaji Ahmad Maiyaki, shi ne ya shugabanci wannan taron bita kuma ya ce dole ne ‘yan jarida su yi taka-tsantsan, saboda yada labarai ba shi ne kadai aikinsu ba, suna da hakki wajen tabbatar da cewa ‘yan siyasa ba sa yaudarar al’umma.

‘Yan jarida da dama ne dai su ka halarci wannan taron bita game da rawar da za su taka a lokacin zabe kuma sun ce sun amfana da taron.

‘Yan jarida da yawa sukan fuskanci barazana daga wasu ‘yan siyasa a lokacin yakin neman zabe, sai dai kungiyar ta NUJ ta yi alkawarin kare mutuncin mambobinta idan dai sun yi aiki kan gaskiya da kuma bin ka’idoji.

Saurari rahoton Isah Lawal Ikara:


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg