Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa Zata Duba Tayin Da Gwamnatin Tarayya Tayi Musu Kafin Su Janye Yajin Aikin Da Suke 


Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa Ta Kasa NARD tace  zata zauna zaman taro a yau domin duba sabon tayin da gwamnatin tarayya tayi musu na biya musu bukatun da suka jawo suka tsunduma yajin aiki a ranar 4 ga watan Satumba. 

Wani wakili a kungiyar Dr Arikawe Adeolu, ne ya bayyana haka jiya a Abuja. Inda yace taron zai bawa kungiyar damar tattaunawa kan batutuwan da suka taso yayin ganawar wakilan kungiyar da tawagar gwamnatin tarayya.

 Adeolu wanda shine babban sakataren kungiyar a Cibiyar Kula Da Lafiya Ta Tarayya dake Jabi a Abuja, yace a abinda aka cimma a karshen taron shine zai nuna ko  za a janye yajin aikin ko kuma za a cigaba har sai baba ta gani. 

Yace duba tayin da gwamnatin tarayya tayi musu ya zama dole saboda kaso 90 na yayan kungiyar basu samu kudin da suke bin bashi ba ya zuwa karfe 3 na yammacin ranar 11 ga watan Satumba.Ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa gwamnatin tarayya zata biya kudin kamar yadda tayi alkawari.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like