Kungiyar Kwadago Za Ta Gudanar Da Zanga-zangar Lumana Kan Batun Tallafin Man Fetur
Shugaban kungiyar kwadago Komred Ayuba Wabba ya ce duk wani yunkuri na cire tallafin man fetur a yanzu, alama ce na kin sauraren talakawa abinda kungiyar ba za ta lamunta ba.

Wabba ya ce kungiyar kwadago na adawa da shirin karin kudin man fetur ta bayan fage, saboda ha’inci da rugujewar siyasar karin farashin man fetur, da gwamnatocin da suka shude a Najeriya suka yi a baya, da kuma gazawar gwamnati mai ci yanzu wajen gyara matatun man kasar.

Wabba yayi karin haske akan shirin zanga-zangar, ya na mai cewa ba yajin aiki ne ba, za su yi zanga-zangar lumana ce saboda tattalin arzikin kasar na faduwa.

To sai dai a wani abu mai kaman mayar da martani, shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya fito fili ya kare wanan batu na cire tallafin man fetur, inda ya bada tabbaci cewa shugaban kasa bai shaida wa kowa cewa za a cire tallafin man fetur ba, kuma sun san cewa tallafin abu ne mai nauyi akan gwamnati.

Bincike ya nuna cewa tsakanin shekara 2012 zuwa yanzu an kashe kusan dalar Amurka biliyan 9.5 wajen gyara matatun man kasar, amma har yanzu shigo da tatatcen man fetur ake yi daga kasashen waje,

Saurari rahoton Medina Dauda cikin sauti:


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg