Kungiyar Daliban Nijeriya Na Kasar Sudan Sun Ziyarci Gidan NakasassuZiyarar zuwa gidan Nakasassu na Musamman mai suna Cheshire Wanda Dr. Abubakar Adamu da Kungiyar matasa Masu bada tallafi ga mabukata mai suna HAAN Foundation mai membobi daga daliban Nigeria masu karatu a jami’o’i daban daban dake Sudan suka kai a yau Lahadi 14/5/2017.

Abin sha’awa shine shi wannan guri ya kunshi ingantattun tsare tsare wanda suka hada da, bada cikakkiyar kulawa da lafiyar nakasassun tare da tsarin ba su ilimi da kuma moya musu sana’o’i daban daban.

Wannan irin guri shi ya dace a ce an gina a kowane juha a Arewacin Nijeriya domin kula da lafiyar Nakasassu tare da ba su cikkakkiyar kulawa, ba kawai a kyale su a kan titina suna bara ba. Hakan ci baya ne ga al’umma.

Allah muke roko da ya ba mu shugabanni masu hangen nesa ba hangen aljuhan su ba, ya kuma kara wayar da kan matasan mu domin gujewa sharrin siyasar raba kudi su ma su tashi su nemi na kansu har ma su taimakawa wasu kamar yadda wannan kungiya ta HAAN foundation Youth For Support take yi.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like