Fitaccen malamin addinin Kirista a Najeriya mai mabiya a sassan duniya TB Joshua ya rasu.

Ya rasu yana da shekara 57 a birnin Legas da ke kudu maso yammacin kasar.

“Allah ya karbi bawansa, TB Joshua.” Wata sanarwa da Cocinsa ta ‘The Synagogue, Church of All Nations’ ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce.

Sai dai sanarwar ba ta fadi musabbabi ko lokacin da shahararren mai wa’azin ya rasu ba, wanda asalin sunansa Temitope Joshua.

“A ranar Asabar, 5 ga watan Yuni, 2021, TB Joshua ya yi jawabi a wajen taron da aka shirya don tattaunawa kan shirin gidan talbaijin na Emmanuel.”

Marigayin na da fitaccen gidan talabijin da yake wa’azi, wanda ake kira Emmanuel TV.

A cewar sanarwar, abu na karshe da malamin addinin Kiristan ya fada shi ne, “ku sa ido, ku ci gaba da addu’a.”

Tun a ranar Asabar jita-jitar mutuwar mai wa’azin ta karade shafukan sada zumunta.

Wani abu da ya sa TB Joshua yin fice a duniya shi ne, ikirarin da ya yi, na cewa yana iya warkar da cututtuka iri-iri, ciki har da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV/AIDS.

Hakan ya sa jama’a daga sassan duniya, kan yi tattaki har zuwa Najeriya don neman waraka.

Katafaren ginin Mujami’arsa da ke Legas ya taba ruftawa a shekarar 2014, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 100 ciki har da ‘yan kasar Afirka Kudu da dama.

An haifi TB Joshua a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1963 – ya rasu kwana shida kafin ya cika shekara 58.