Kudurin dokar wacce mataimakiyar mai tsawatarwa a Majalisar Wakilai daga Jihar Abia, Nkiru Onyejiocha ta kawo, ya samu hadin gwiwar ‘yan Majalisar 100 cikihar da shugaban Majalisar Wakilan Femi Gbajabiamila.

Wannan dokar na neman a canja sashi 48 na Kundin tsarin mulkin kasa da zai sa a samu kujeru hudu a Majalisar Dattawa, wato Sanatoci uku daga ko wacce Jiha kuma daya daga babban birnin taraiyya Abuja wanda za su kasance mata.

A yanzu mata 8 ake da su a Majalisar Dattawa, sannan 13 a Majalisar Wakilai wanda ya ke nufin kashi 4.4 a cikin dari ne kacal ke Majalisar.

Malami a tsangayar siyasa da diflomaciyar kasa da kasa a Jami’ar Baze, Farfesa Usman Mohammed yana ganin wanan kudurin ba mai yiwuwa ba ne domin mata sune matsalar mata yan uwan su.

Farfesa Usman ya ce mata kashi 70 ne ke zabe kuma ba sa zaben mata ‘yan uwansu, kuma sukan yi gaba da juna har ba sa ga maciji, wannan alama ce ta cewa abin ba zai yi nasara ba. Farfesa Usman ya ce shi ba ya goyon bayan wannan doka domin za a ba ‘yan Najeriya wahala ne kawai domin zata bukaci a canja kundin tsarin mulki.

To saidai mata da suka dade suna kokarin a ba su kashi 35 cikin 100 na kujerun siyasa ko mukamai suna ganin wannan doka za ta zo akan gaba, Hajiya Mariya Ibrahim Baba, gogagiyar ‘yar siyasa ce da ta taba tsayawa takarar Kujerar Mataimakin Shugaban Kasa, ta baiyana ra’ayin ta cewa abun alfahari ne, domin tana ganin lallai lokaci yayi da ya kamata a dama da mata a dukanin harkokin siyasa, inda ta yi fatan za ta mora ita ma, kuma za ta yi kokarin jan hankalin mata matasa domin su shiga harkar siyasa gadan gadan saboda a samu ci gaba a kasar.

Ita ma Hajiya Hauwa Bukar wace ta taba rike mukamin shugabar Mata a shiyar Arewa maso Gabas, ta ce ta yi farin cikin jin wannan yunkurin da Majalisar kasa ke yi. Hauwa Bukar ta ce su mata yan siyasa sun dade suna neman wannan dokar, kuma ana yi a kasashe irin su Indiya wadanda suka fi Najeriya yawan al’umma, saboda haka abu ne mai kyau Najeriya ta yi koyi da shi saboda a dama da mata.

Idan an yi dokar, mafi karancin mata a Majalisar Dattawa za su zama 37 a cikin mutane 109, sannan a Majalisar Wakilai kuma za su zama 74 a cikin yan Majalisa 360. Yanzu haka dai dokar ta shiga karatu na biyu a Majalisar Wakilai.

Domin karin bayani saurari rahotan Medina Dauda.